Siyasa

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na bunkasa shaanin tsimi da tanadi domin bunkasa sana’o’i a fadin Jihar

 

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na bunkasa sha’anin tsimi da tanadi domin cigaban tattalin arzikin jihar nan.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya jaddada hakan yayin da ayarin jam’iyyun gama kai da tsimi da tanadi suka kawo masa ziyarar ban girma da neman tubarraki karkashin jagorancin shugabanta Musa Hassan Aikawa a ofishinsa dake fadar gwamnatin jihar Kano.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar zasu shigo da gamayyar kungiyoyin hada kai da tsimi da tanadi wajen kawar da talauci a jihar nan.

Sannan kuma ya kara da cewa, zasu horas da matasa harkokin tsimi da tanadi domin bunkasa sana’o’i da walwalar matasa a fadin jihar nan.

Kazalika, mataimakin gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsu zata sanya harkokin tsimi da tanadi a cikin tsare-tsaren ta domin samun cigaba mai dorewa.

Shima anasa bangaren Shugaban kungiyar gamayyar hada kai da tsimi da tanadi na jihar nan musa Hassan Aikawa ya bayyana cewar an kafa wannan kungiyar ne a shekarar 1952 wadda a wannan lokacin kaso casa’in da tara na ‘ya’yanta manoma ne wadda aka kafa ta domin magance asasar da manoma keyi a Arewacin Kasarnan ta yadda idan suka hada kansu za’a samu kamfanin da zai sayi amfanin gonarsu.

Ya kuma bayyana cewar, kawo wa yanzu jihar Kano ta na kungiyoyin gama kai miliyan biyu da dari bakwai wanda mafi akasarin su matasa ne.

Daga cikin mahalarta taron akwai Babbar Sakatariyar ma’aikatar kasuwanci da masana’antu Hajiya Mairo Audi Dambatta da Shugaban Kwalejin koyar da aikin gona ta tarayya Dakta Muhammad Yushau.

Leave a Comment