Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na Bunkasa Sha’anin Noma a fadin jihar

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ne ya furta hakan a yayin kaddamar da tallafin kayayyakin noma na gwamnatin tarayya wanda ya gudana a garin Bunkure dake karamar hukumar Rano.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar noma shi ne kashin bayan cigaban tattalin arzikin kowacce al’umma da samar da abinci, aikin yi da kuma inganta walwalar miliyoyin al’umma.

Ya kuma bayyana cewar shirin wanda gwamnatin tarayya ta bijiro dashi ta hanyar hadin gwuiwa da jihohin da zasu ci gajiyar shirin da kuma gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki masu zaman kansu zai farfado da sha’anin noma a fadin kasarnan.

Ya kuma kara da cewa jihohin da shirin ya shafa sun hadar da Kano, Jigawa, Niger, Sokoto, da kuma jihar Kebbi.

Kazalika yace, daga cikin al’ummomi 36 da zasu amfana da kayayyakin tallafin a jihar nan sun hadar da Bunkure, Rano, Dawakin Kudu, Bagwai, Bebeji da kuma Garun Malam.

Daga cikin kayayyakin tallafin akwai takin zamani irin shuka maganin Kwari da ciyawa da sauran kayayyaki.

Shima anasa bangaren wani Darakta a ma’aikatar gona wanda ya wakilci babban Sakataren ma’aikatar Alhaji Bukar Musa ya bayyana cewar sama da manoma dubu saba’in ne daga kananan hukumomi ashirin da shida na kasarnan ne zasu ci gajiyar shirin.

Wakilinmu na Ofishin mataimakin gwamnan jihar ya ruwaito cewar daga cikin mahalarta taron akwai babban Sakataren ma’aikatar gona da dan majalisar jiha mai wakiltar yankin da Shugaban kwamitin aikin gona na majalisar dokokin jihar nan da hakimin yankin da Shugaban karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin noma.

Leave a Comment