Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na yin aiki kafada da kafada da ‘yan yiwa Kasa hidima wajen ciyar da sha’anin ilimi da lafiya gaba a Jihar.

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na cigaba da samar da tsaro da kare lafiyar ‘yan yiwa kasa hidima da aka turo domin hidintawa jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da ‘yan yiwa kasar hidima rukuni na biyu na wannan shekarar a sansanin su dake Kusalla a karamar Hukumar Karaye.

Mataimakin gwamnan kuma Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masauratu na jihar nan ya bayyana cewar zasu yi aiki kafada da kafada da ‘yan yiwa kasa hidimar wajen ciyar da sha’anin ilimi da kiwon lafiya gaba a fadin jihar.

Ya kuma bayyana cewar yana mai tabbatarwa ‘yan yiwa kasa hidimar basu kariya don haka ya bukace su da su kwantar da hankalin su su zauna da kowa lafiya kasancewar al’ummar jihar nan mutane ne masu karrama baki.

Shima anasa bangaren jami’in gudanar da shirin ‘yan yiwa kasa hidima na jihar  sulaiman Andu Ibrahim ya bukaci ‘ya’yan hukumar su zamto masu bin doka da oda yayin gudanar da aikinsu.

Ya kuma kara da cewar yanzu haka sun karbi yan yiwa kasa hidima rukuni na biyu na wannan shekarar su kimanin dubu daya da dari tara a fadin jihar nan.

Wakilinmu na ofishin mataimakin gwamnan jihar Shehu Suleiman Sharfadi ya ruwaito cewar daga cikin mahalarta taron akwai kwamishinoni da mataimakin kakakin majalisar dokoki da wakilin Sarkin Karaye.

Leave a Comment