Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Rungumar Kungiyoyi Asu Zaman kansu da ke da urin Bunkasa Rayuwar Al’ummar Jiharnan

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI
Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusif ya furta hakan a yayin da kungiyar bunkasa cigaban kasashen rainon ingila mai suna Blue Sapphire Hub ta gabatar masa da rahoton da ta kammala kan yadda zaa yi kirkira da bunkasa shaanin ilimin yanar gizo a fadin jihar nan.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar shaanin ilimin yanar gizo bangare ne da ya shafi dukkan lamura na rayuwa ba ga mutumin kauye ba ko na birni ko talaka ko mai kudi ko mai ilimi ko mara ilimi da kuma bunkasar tattalin arziki na Zamani.

Ya kuma baiwa kungiyar tabbacin hadin kai da goyon baya daga gwamnatin jihar nan.

Itama anata bangaren Shugaban kungiyar Hajiya Maryam Gwadabe ta bayyana cewar sun kawo ziyarar ne domin mikawa gwamnati rahoton da suka kammala wanda suke so gwamnati tayi aiki dashi a cikin tsare tsaren ta da kuma sauya fasalin shaanin yanar gizo ta yadda zai amfani kowa a fadin jihar nan.

Ta kuma shawarci gwamnatin jihar nan kan cewar muddin gwamnati ta yi amfani shawarwarin da suka bayar to tabbas jihar Kano sai tayi nisa a bangaren tattalin arziki na Zamani.

Shima anasa bangaren jamiin gudanar da shirin na jihar Kano Umar Fari ya bayyana cewar wannan rahoto nasu da suka kammala hadin gwiwa ne da masu ruwa da tsaki a bangarori da dama da ya kunshi muhimman shawarwari da kirkire kirkire kan yadda zaa bunkasa shaanin ilimin yanar gizo tun daga tushe domin bunkasa tattalin arziki na Zamani a fadin jihar Kano.

Wakilinmu na Ofishin mataimakin gwamnan jihar nan Shehu Suleiman Sharfadi ya ruwaito cewar,

taron ya samu halartar Kwamishinan ma,aikatar kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire na jihar nan Alhaji Tajuddin Usman da Sakataren gwamnati da kuma sauran kwamishinoni.

Leave a Comment