Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano Ta Gudanar Da Auran Gata ga Maraurata 1800

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin Jihar Kano Ta Gudanar Da Auran Gata ga Maraurata 1800

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci ma’auratan dasu ka rabauta da auran gata wanda gwamnatin jihar Kano ta kaddamar a yau Juma’a a babban masallacin jumaa na jihar Kano su kimanin 1800 dasu zauna lafiya da matayensu kamar yadda koyarwar addinin musulunci ta shar’anta.

gwamnan yaja hankalin maauratan da cewa su saka tausayi da tsoron Allah wajen kulawa da matayansu.

Gwamnan ya kara da cewa wannan shine karo na farko da wannan gwamnati tayi tun bayan da gwamnatii engr Rabiu Musa Kwankwaso wa’adinta ya shude.

Ya kuma bukaci maauratan musamman matan dasuyi biyayya ga mazajensu don samun da cewa a gurin Allah Subahanahu Wata’alah.

limamin jihar kano farfesa Sani zaharaddeen ne ya jagoranci daurin auran.

Kwamandan Hisba na jihar kano Aminu Ibrahim Daurawa yaja hankalin ma’auratan dasu rike junansu da gaskiya da amana don samun da cewa da zuri’a dayyiba.

wakilimmu Adamu Dabo D/tofa ya rawaito mana cewa tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci shaida daurin auren da sauran al’umma da suka fita daga jahohi daban daban.

Leave a Comment