Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bukaci Tubabbun ‘Yan Dabar Da Suka Ajiye Makamansu Su Zamu Masu Son Zaman Lafiya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci tubabbun ‘yan dabar da suka ajiye makamansu da suzo a hada kai dasu don kara samar da zaman lafiya a jihar Kano.

Gwamna Abba kabir Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yayi taron taya tubabbun murnar zama jakadu na gari a rufaffen dakin taro dake sitadiyom din Sani Abacha Kofar Mata.

Gwamnan ya kara da cewa a shirye gwamnati take ta dauki nauyin dukkan Wanda zai koma makaranta tun daga matakin firamare har zuwa jami’a.

Ya kuma bayyana cewa, nan da mako biyu za’ayi bikin basu tallafi da kuma koya masu Sana’oi’n dogaro da kai
daga bisani ya yabawa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Muhd Usaini Gumel.

Da yake nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kanon yayi kira ga malamai da al’umma dasu cigaba dayi musu addu’a da kuma jansu a jiki batare da nuna masu banbanci ba.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar ya ruwaito mana cewa sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya yabawa da gwamnatin jihar Kano da kwamishinan ‘yan sanda bisa yadda sukayi tunanin don samun dorewar da zaman lafiya a jihar.

Leave a Comment