Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano Na Taya Al’ummar Kasarnan Murnar Cikar Najeriya Shekaru 63 Da Samun ‘Yanci

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Mataimakin gwamnan jihar kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo na taya daukacin al’ummar kasarnan murnar cikar Najeriya shekaru 63 da samun mulkin kai.

A cikin sanarwar da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan ya fitar Ibrahim Garba Shuaibu yace wannan rana lokaci ne da yan Najeriya zasu yi farin ciki da murnar zagayowar ta tun daga ranar da kasarnan ta samu yanci

Mataimakin gwamnan ya bukaci al’ummar Kasarnan suyi aiki tare domin gina sabuwar Najeriya.

Gwarzo, ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga yan Najeriya kan su rungumi zaman lafiya, inda yace Kasarnan ba zata taba shahara ba sai ta hanyar hadin kai da kuma yin aiki tare ga al’ummar kasarnan.

Leave a Comment