Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano Na Mika Sakon Ta’aziyarta Ga Al’ummar Karamar Hukumar Bagwai Bisa Rasuwar Alhaji Muntari PA

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Muntari Musa PA a karamar hukumar Bagwai.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 59 ya kuma bar mata uku da yaya goma sha biyar.

Mataimakin gwamnan ya kwatanta rasuwar Alhaji Muntari a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma da daukacin al’ummar musulmin jiharnan.

Daga nan sai yayi masa addu’ar samun rahama a gurin Allah tare da baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Da yake tarbar mataimakin gwamnan, Shugaban karamar hukumar Alhaji Inuwa Zangina Dangada ya godewa mataimakin gwamnan bisa wannan ziyarar ta’aziyya da ya kawo musu.

Leave a Comment