Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Bada Tallafin Naira Miliyan Daya Ga Kowanne Maniyyaci

Written by Admin

Daga: Kabir Getso 

Gwamna Umar Mallam Namadi ya amince da baiwa maniyatan aikin hajjin bana tallafin naira miliyan dai dai domin samun damar cika Karin kudaden kujerar aikin hajjin bana.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin Hukumar aikin hajji ta jiha Murtala Usman Madobi ya sanyawa hannu ina ya rawaito shugaban Hukumar Ahmed Umar Labbo na cewar sakamakon hakan, a yanzu maniyatan jihar Jigawa zasu cika naira dubu dari tara da goma sha takwas da naira talatin da biyu da kobo casa-in da daya.

A yanzu haka dai hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta sayar da kujeru 1,260 daga cikin kason da hukumar aikin hajji ta kasa ta bata na kujeru 1,518.

Sanarwar ta bukaci maniyyatan da su yi amfani da wannan dama wajen samun damar sauke farali a kasa mai tsarki.

Leave a Comment