Yanzu-Yanzu

Gwamnati ta rubanya kokarinta wajen bunkasar kwalejojin Lafiya – Hamza

By: KABIR GETSO

Mataimakin Shugaban Kwalejin lafiya ta Birnin Kudu dake Jihar Jigawa (College of Nursing and Sciences) Alh Hamza Abubakar. Ya bayyana Kwalejin a matsayin wata garkuwa ga al’ummar kasar nan wajen samar da Nagartattun Dalibai masu sanin makamar Ilimin lafiya.

Alh Hamza Abubakar wanda shine ya wakilci shugaban kwalejin a lokacin tattaunawa da manema labarai a Kwalejin, yace idan akayi la’akari da mahimmancin karatun lafiya yana da kyau Gwamnatoci su rubanya kokarinsu na inganta kwalejojin.

Ya kara da cewa, saboda kwazon Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar yasa dukkanin kwalejojin jihar ke zama abin koyi ga saura wanda hakan yasa Dalibai da dama ke samun sukunin lashe jarabawa a bangarori da dama na kwalejin.

Ya kara da cewa a baya kwalejin tana dibar Dalibai matsaikaita amma yanzu abin ya haura hakan saboda samun damar bude wasu sabbin resuna a Hadejia da Babura.

Malam Hamza ya yabawa Gwamnatin Jihar Jigawa karkashin Shugabancin Gwamna Badaru Abubakar, bisa irin kokarinsa na samawa kwalejin kayan aiki da sabbin gine gine domin dorewar bunkasar kwalejin don anfanuwar al’ummar jihar dama kasarnan baki daya.

Shugaban kwalejin ya ja hankalin Daliban da su kasance jakadu nagari wajen aiki tukuru da maida hankali don dorewar cigaban Kwazon kwalejin a idon al’umma, tare da kaucewa duk wata mummunar dabi’a da zata zub da darajar kwalejin a idon duniya.

Kazalika ya yi kira da sauran masu rike da madafun iko da sauran masu hannu da shuni da su Cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen kokarin tallafa kwalejin a fannoni da dama.

Leave a Comment