Siyasa

Gwamnan Jihar Kano Ya Yabawa Gwamnan Katsina Akan Inganta Harkokin Tsaro

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya ce zasu hada hannu da gwamnatocin jihohin arewa maso yammacin kasar nan domin inganta tsaro a yankin.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron kaddamar da jami’an tsaro na musamman da motoci masu silke da gwamnan jihar katsina Dr. Umar Dikko Radda ya samar domin inganta tsaro a jihar wanda aka gudanar a filin wasa na Muhammad Dikko dake jihar Katsina.

Ya bayyana gamsuwarsa bisa tsarin gwamnatin jihar na horas da matasa dabaru da al’amuran tsaro.

Yace matasan da aka horas kimanin 1450 wanda gwamnatin jihar ta zabo su daga sassan jihar dake fama da matsalolin tsaro, zasu bada gudummawa wajen dakile ta’addanci da aikata miyagun laifuka a fadin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa gwamnatocin yankin arewa maso yammacin kasar nan sun kuma tattauna hanyoyin da zasu habaka tattalin arziki da harkar noma a jihohinsu.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano adamu Dabo ya bamu labarin cewar taron ya samu halartar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da gwamnonin Johohin Yobe da Zamfara da Sokoto da kuma jihar Kebbi .

Leave a Comment