Labaran Jiha

Gwamnan jihar Kano ya Sanya Hannu Akan Kasafin Kudi Na 2023

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kwaryakwaryar kasafin kudi na shekarar 2023 wanda ya haura sama da naira biliyan hamsin da takwas da miliyan dari da casa’in da daya.

Yayin da yake sanya hannun kan kasafin, Gwamnan ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta bi ka’idoji wajen aiwatar da kasafin kudin bisa gaskiya da adalci.

Ya kuma yaba wa kwamishinan kasafi da tsare-tsaren kudi bisa kokarin da yayi wajen gaggauta gabatar da kasafin kudin ga majalisar jiha.

Abba Kabir Yusuf ya kuma bada tabbacin ci gaba da bada goyon baya da aiki gidan gwamnati.

Leave a Comment