Labaran Jiha

Gwamna Yusuf Ya Rantsar Da Shuwagabannin Rikon Kwarya Na Kananan hHukumomi Arba’in Da Hudu

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jahar Kano ta ja hankalin shuwagabannin riko na kananan hukumomi arba’in da hudu da su zama masu gaskiya da rikon amana wajen gudanar da aiyukansu.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin bikin rantsar da shuwagabanin riko na kananan hukumomi arba’in da hudu wanda aka gudanar a dakin taro na coronation dake gidan gwamnati.

Gwamna Yusuf ya bukaci shugabanin da su zamo masu amana da gaskiya da kuma zuwa ofis akan lokaci don gudanar da ayyukan al’umma cikin nasara.

Daga bisani ya umarce su dasu shiga ofis ranar litinin su kuma rantsar da mataimakansu da sakatarorinsu gami da kansilolin riko, ya kuma ce suna da waadin watanni uku kamar yadda doka ta tanadar.

Kwamishinan shari’a na jahar Kano Barista haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da shuwagabannin rikon kwarya na kananan hukumomi arba’in da hudu.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano murtala Adamu Dabo ya rawaito mana cewa a yayin bikin rantsuwar a akwai mataimakin gwamnan jihar Kano Wanda kuma shine kwamishinan kananan hukumomi Aminu Abdulsalam gwarzo da s kwamishinonin gwamnatin jahar Kano.

Leave a Comment