Yanzu-Yanzu

Gwamna Yusuf Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Karamar Hukuma

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Sabon shugaban karamar hukumar Bebeji Alhaji Ali Ibrahim kuki, tare da rantsar da sabbin masu bawa Gwamna shawara akan ayyuka daban-daban na gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci karbar rantsuwar ta hannun Barrister Haruna Isah Dederi a fadar gwamnatin jihar Kano.

A yayin rantsaruwar gwamna Yusuf ya rantsar da manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati guda 21 da Kuma masu Bada shawara na musamman guda 15.

Ya kuma basu shawara da su zama masu gaskiya da rikon amana domin samun cigaban jihar Kano.

Daga karshe taron ya samu halattar tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kano farfesa Hafizu Abubakar da kwamishinoni da manya da kananan ‘yan siyasa dake fadin jihar Kano.

Leave a Comment