Labaran Jiha

Gwamna Yusuf Ya Karbi Shuwagabannin Kananan Hukumomi Uku

Written by Admin

 

Gwamnan Kano ya karbi shuwagabannin kananan hukumomi uku daga jam’iyar APC zuwa jam’iyar NNPP

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karbi shuwagabannin kananan hukumomin uku daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP.

Gwamna Yusuf, ya karbi shugaban karamar hukumar Nasarawa Hon. Auwal Lawan Aramposu, Ado Tambai Kwa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa da Kuma Mudassir Aliyu shugaban karamar hukumar Garun Malam.

Bikin karbar ta su ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar Kano.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano ya ruwaito cewa, a yayin bikin karbar shuwagabannin kananan hukumomin akwai mataimakin gwamnan jihar Kano Comr. Aminu Abdulsalam da sauran ma yan kusoshin jam’iyar NNPP.

Leave a Comment