Da Dumi-Dumi

Gine-ginen Tashar Malam Kato ya raba Direbobi da dama da sana’arsu. N.U.R.T.W

From: IBRAHIM SANI GAMA

Hukumar gudanarwar kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen Jihar Kano dake Tashar mota ta Malam Kato, ta koka da yadda aka siyar da Tashar tare da gineta ba bisa kaida ba da Gwamnatin da ta gabata ta yi.

Shugaban yada labarai na kungiyar Alhaji Samaila Giredi ne yayi kokawar lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, dangane da halin da ‘ya’yan kungiyar suka tsinci kansu a ciki.

Alh. Samaila Giredi, ya bayyana cewa, sakamakon gine wajen da aka yi, ya sanya wasu motocin sun fito wajen Tashar domin neman gurin tsayawa, inda matasa da dama da magidanta sun rasa hanyoyin cin abincinsu, wanda haka ba karamar matsala bace ga rayuwar al’umma.

Yace, tashar Malam Kato, tsohon Gwamnan jihar Kano, DR. Rabiu Musa Kwankwaso ne, wanda ya samar da ita sakamakon taso direbobi daga shataletalen Bata domin su bar kan hanya, amma ga shi Gwamnatin da ta gabata ta cefanar da Tashar.

Samaila Giredi ya bayyana cewa, Tashar, Tashace da baki suke zuwa domin hawa mota dan yin tafiye-tafiye kamar kasuwar Singa, Sabon Gari da Kofar Wambai da kuma, sauran kasuwanni dake fadin Jihar Kano.

Yace yanzu haka ba by wata tasha da take daukar fasinja ko kayayyaki, wanda yace, dukkansu gwamnatin Jihar Kano da ta gabata ta siyarwa wasu mutane masu hannu da shuni, yin haka na nuni da cewa babu tausayi ga masu karamin karfi da suke cin abinci a wannan Tasha.

Shugaban ya roki Gwamnatin jihar Kano da take kwatowa wadanda aka zalunta hakkokinsu, da ta waiwaya domin tunawa da Tashar kasancewar kungiyar ta baiwa Gwamnatin cikakken goyan baya har Allah yasa aka kafa wannan Gwamnati, inda ya bukaci da a kawo Tashar daukin gaggawa domin fitar da bayin Allah daga cikin damuwa ta yau da ta gobe.

Alhaji Samaila ya ayyana cewar, an fara yin gine ginen ne watanni biyu kafin zabe tare da gayyato masu gini kimanin guda Dari ne suke gudanar da ayyuka a kullum domin ganin an kammala cikin Dan lokacin kalilan, wanda hakan ba karamar barazana bace ga Al’ummar dake ci abinci a gurin.

Haka zalika kungiyar tace, ba za ta gajiya ba wajen yin kiraye kirayen Gwamnati mai ci karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, tunatar da ita duk da cewa, kungiyar tasan maigirma Gwamnan Jihar Kano da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da shugabannin da alhakin karbowa al’umma hakkokinsu ya rataya akansu.

Kungiyar ta jaddada cewa, a shirye take wajen ci gaba da baiwa Gwamnati cikakken goyan baya da hadin kan daya kamata, musamman domin dawowa da talakawa dukiyarsu.

Alhaji Samaila Giredi yace, dubbannin al’umma ne suke cin abinci a wannan Tasha, saboda fito da su da aka yi,ya haifar da matsaloli cinkoson ababan hawa,Wanda wannan na daga cikin hangen nesa da DR. Rabiu Musa Kwankwaso ya duba, direbobin da motocinsu ya mayar da su cikin Tashar Malam Kato sama da shekaru Ashirin da suka gabata.

Daga karshe kungiyar ta yabawa Gwamnati, bisa namijin kokarin da take yi na ganin ta karbowa al’ummar Kano hakkokinsu da aka kwace ba tare da an samar musu da mafita ba domin dogaro da kawunansu da rage masu zaman kashe wando a tsakanin al’umma wanda rashin sana’a yana haifar da gagarumar matsala da aikata abubuwa marasa kyau.

 

 

Leave a Comment