Labaran Jiha

Gidauniyar KANAWA Ta Tallafawa Masu Bukata Ta Musamman Da Kayan Sallah

Written by Admin

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu

Gidauniyar tallafawa ilmin masu bukata ta musamman wato KANAWA EDUCATION FOUNDATION FOR PEOPLE WITH DISABILITIES ta tallafawa masu bukata ta musamman sama da Dubu da kayan abinci da Kuma kayan sallah a nan Kano da ma wasu jihohi.

Shugaban kungiya Malam Ibrahim Garba Magami yayin kaddamar da rabon tallafin a nan Kano ya ce manufar kungiyar shi ne domin sanya farin ciki a zukatan wadannan bayin Allah musamman a wannan wata na Azumin Ramadana da kuma shugulgulan bikin karamar Sallah da ke tafe.

Malam Ibrahim Garba ya ce gidauniyar ta Kuma tallafawa masu bukata ta musamman da wasu marasa gata da tallafin kudin magani a Asibitoci.

Shugaban kungiyar ya Kuma ja hankalin Al’uma musamman mawadata da su Kara kasancewa masu tallafawa irin wadannan mutane domin suma mutane ne kamar kowa.

Malam Ibrahim Garba ya kuma bukaci gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da ya amince da nada shugabannin hukumar kula da masu bukata ta musamman a kokarin da ake na ganin hukumar ta fara aiki tun bayan amincewa da kafa hukumar da majalisar Dokoki ta jihar Kano ta yi.

Leave a Comment