Labaran Jiha

Ganduje Ya tura Sunan Ali Burum-Burum Majalisa don Nada shi Kwamishina

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muhammad Adamu Abubakar

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tura Sunan Dakta Ali Musa Burum-Burum ga majalisar dikin jihar Kano domin tantance shi da nufin nada shi mukamin Kwamishina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari a madadin Gwamnatin jihar Kano.

Wata sanarwa da daraktan yada labaran majalisar ya aikowa Pyramid Radio, ta bukaci Ali Burum-Burum da ya ziyarci majalisar ranar litinin 22 ga watan Ogustan 2022 lokacin da sauran wadanda aka tura Sunan su zasu ziyarci majalisar domin tantancewa.

Idan zaa iya tunawa dai a jiya litinin ne Ganduje ya tura sunayen mutane takwas domin tantance su tare da amincewar su domin nada su mukaman kwamishinoni.

Leave a Comment