Yanzu-Yanzu

Eid El Fitr: Sarkin Rano ya bukaci a cigaba da Darussan Ramadan.

 

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

 

Maimartaba Sarkin Rano Dr Kabir Muhammad Inuwa Autan Bawo ya hori al’umar musulmi da su cigaba da aiwatar da ladubban da suka koya lokacin Azumin watan Ramadan da ya gabata bayan sallah.

Mai martaba sarkin ya yi horon ne a sakonsa na barka da sallah ga al’umar yankin masarautar Rano da sauran al’ummar musulmi bayan kammala sallar Idi a babban masallacin Idi na Rano. Ya kuma bayyana godiyarsa ga Sarki Allah (Subhanahu Watta’alah) bisa yadda Al’ummar Musulmi da suka kammala Azumin Ramadam a bana.

Maimartaba Sarkin Rano Dr. Kabir Muhammad Inuwa ya kuma yi Addu’ar Allah Ya karbi dukkan ibadun Al’ummar Musulmi.

Ya kuma tunatar da shugabannin Al’umma da su kara kulawa da halin da Al’umma suke ciki la’akari da halin kuncin rayuwa ta hanyar tallafawa mabukata wajan samar masu da aikin yi da matasa da inganta samar da Wadataccen takin zamani ga manoma musamman a wannan lokaci da ake dab da shiga lokacin damina.

Sannan Maimartaba Sarkin ya yaba wa mawadata a yankin dake tallafawa Al’umma inda ya yi masu addu’ar fatan alkhairi. Ya kuma hori sauran al’umma da su yi koyi da haka.

Daga nan ya mika godiya ga Gwamnatin Jahar Kano wajen yadda ta samar da ayyukan raya kasa musamman daga darajar asibitin Rano ya kuma yi wa sabbin shugabanni a matakai daban-daban da aka zaba murna tare da yi musu fatan alkairi.

Shima Babban Limamin masallacin Idin na Rano da ya jagoranci Sallar Imam Kabir Muhammad Sani ya bayyana muhimmancin Zakkar Fiddakai a tsakanin Al’ummar musulmi.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai da kasa Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya wakiltar ya bukaci al’umma da su cigaba da zama da junansu lafiya a ko da yaushe.

Leave a Comment