Labaran Jiha

Dokar Masu Bukata ta Musamman: Muna Yabawa Gwamnatin Kano — Saifullahi Muktar

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Gidauniyar tallafawa ilimin masu bukata ta musamman ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa samar da dokar masu bukata ta musamman da nufin kare muradansu.

Daya daga cikin jagororin gidauniyar Malam Saifullahi Muktar ne ya sanar da haka yayin taron ranar masu bukata ta musamman ta bana a nan Kano.

Ya ce yabon ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda suke ta fadi-tashi domin ganin an samar da dokar a dukkanin jihohin kasar nan a kokarin da ake na inganta rayuwar masu bukata ta musamman.

“Samar da wannan doka da gwamnatin jihar Kano ta yi da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya Sanya wa hannu a makon da ya gabata abin a yaba ne matuka, a don haka za mu Kara zage Dantse domin ganin an fara aiwatar da ita musamman kafa hukuma da ayyukanta zai kasance domin kula da masu bukata ta musamman”, inji Saifullahi Muktar.

Ku karanta: Muna Bukatar Tallafin Iyaye, Dattawa da Gwamnatin Don Gina Matsuguni na Din-Din-Din — Shugaban B. I. T.

Ya kuma lasafto kadan daga ayyukan gidauniyar wato _KANAWA EDUCATIONAL FOUNDATION FOR THE DISABLED_ a turance da suka hadar da samar da ilimi tun daga tushe har zuwa manyan makarantu kyauta da koyar da sana’o’in dogaro da kai ta hanyar hadin guiwa da gwamnatoci a dukkanin matakai da kuma wasu kungiyoyi masu zaman Kan su a nan ciki da wajen jihar kano.

A jawabinsa, jami’in hulda da jama’a na cibiyar bai wa matasa horo ta Sani Abacha wanda ita ta shirya taron Malam Yakubu Shu’aibu Ungogo ya bayyana yadda cibiyar ke bai wa masu bukata ta musamman fifiko a duk al’amuranta.

Ya ce a lokacin Shirin bayar da tallafin Noma na Babban Bankin kasa, cibiyar ta Sani Abaca ta bukaci masu bukata ta musamman su biya naira dubu 5 ne kawai sabanin naira dubu 17 da dari 5 domin shiga Shirin.

Ku Karanta: Zamu Goyi Bayan Duk Jam’iyar Da Zata Karbo Hakkin Yan Kungiyar Mu da Aka kashe — Mustapha Ali

A zantawa da manema labarai, wasu daga cikin masu bukata ta musamman da suka halarci taron sun yaba bisa ware musu rana guda domin tunawa da su.

Majalisar dinkin duniya ce dai ta Ware duk ranar 3 ga watan disambar kowacce shekara domin bikin ranar masu bukata ta musamman a ko’ina cikin Duniya.

Leave a Comment