Da Dumi-Dumi

Direbobi da Dama sun rasa sana’arsu sakamakon siyar da Tasha da Gwamnatin da ta gabata ta yi

From: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar direbobi ta kasa reshen Jihar kano, ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin injiniya Abba Kabir Yusuf, daya waiwayi Tashar Malam Kato domin dawowa da al’ummar da suke gudanar da sana’arsu a cikinta, wadanda kimanin mutane dubu biyu ne masu cin abinci a ciki.

Sakataren kungiyar matuka motocin haya ta kasar nan kuma sakataren Kwankwasiyya na kungiyar Kasuwar Singa Alh. Balarabe Ahmed ne ya bukaci hakan dangane da yadda rashin tashar yake haifar da cinkoson ababen hawa a wajen tashar zuwa Kasuwar Bata.

Balarabe Kwankwasiyya ya bayyana cewa, wadan nan direbobin na daya daga cikin mutanen da suka baiwa Gwamnati mai ci gudunmawa domin ganin an kafa Gwamnatin, amma gashi sun koma yadda suke a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Dr. Rabu Musa Kwankwaso daya taimakawa kungiyar suka dawo cikin Tashar Malam Kato domin yin amfani da ita.

Ya bayyana cewa, magidanta da matasa da dama ne ke sana’a a cikin tashar amma sakamakon siyar da tashar da Gwamnatin da ta gabata ta yi asirin wasu da yawa ya tonu da su da iyalansu.

A don haka, kungiyar ta kara tunatar da Gwamnatin jihar cewa, duk da bukatar da gwamnatin ta yi na dakatar da duk wasu gine-gine a guraren dake mallakin Gwamnati, amma hakan ba ta sauya zani ba domin kuwa ko a yau sai da ma’aikatan dake gine-ginen suka ci gaba da aiki.

Balarabe Kwankwasiyya yace, yin hakan kamar karya umarnin gwamnatin ne, da kuma raina hukunci da yin fatali da sanarwar da gwamnatin Injiya Abba Kabir Yusuf ne.

Saboda haka, kungiyar take kara kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin gine-gine da Kwamishinan harkokin sufurin Jihar Kano da Shugaban Hukumar KANUPDA, da su kawowa Kungiyar daukin gaggawa domin fitar da dubban al’umma daga cikin damuwa.

Idan za’a iya tunawa gwamnati mai ci ta yi kiraye-kiraye da mutane su daina siyan kayan gwamnati domin hakan ba zai haifar da ‘Da mai ido ba.

A jawabinsa, shugaban jin dadi da walwala na kungiyar Alh. Samaila Giredi, ya bayyana cewa, yanzu haka wadanda aka siyarwa Tashar sunanan suna gini ba dare ba rana domin su yi saurin kammala wannan aiki.

Haka zalika yace, don Allah, ya kamata Gwamnatin Jihar Ano kano ta kawowa wadan nan mutane da suke gudanar da sana’arsu a cikin tashar daukin gaggawa.

Leave a Comment