Siyasa

Dawo Da Tsarin Mulkin Firaminista Abu Ne Mai Kyau A Nigeria – Hon Dr. Auwal Boss

Written by Admin

Daga: Kabir Getso

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar gundumar Katagum Hon. Dr. Auwalu Abdu Gwadabe Boss ya bayyanna cewar dawo da tsarin mulkin Firaminista a kasarnan abu ne da zai kawo kyara da farfado da tattalin arzikin kasar.

Dr. Auwalu Boss ya bayyanna hakane lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa dake Azare, yace idan akayi la’akari da irin cigaban da aka samu a tsarin mulkin Firaminista na farko duk da anyi shi a takaitaccen lokaci zaiyi wuya a kwatanta shi da irin halin da ake ciki yanzu. “Domin kuwa, mafi yawan kudaden da suke zurarewa a halin yanzu Sunfi tafiya ne a kunshi shugabancin kasar mai makon ayyukan da al’ummar kasar zasu amfana injishi”

Ya kara da cewa, yanzu haka wannan kudiri ya tsallake karatu na biyu a majalisa kuma yana daya daga cikin na gaba gaba wajan samar da wannan kudirin kuma da yardar Allah zai samu sahalewa daga kunshin Majalisar Tarayya kasar nan.

Dr. Auwalu Boss ya kara da cewar cikin watanni 8 da suka gabata da zabar sa’a matsayin dan majalisa ya samar da ayyuka da dama wadanda suka hada da raba Babura, Motoci, Kekunan Dinki, Injinan Taliya da kuma magunguna a dukkanin mazabun dake cikin gundumar Katagum da sauran manyan Ayyukan da lokaci bazai bari a zayyanosu ba kuma irin wadanda ayyukan zasu cigaba da wakana yadda ya kamata.

Ya kara da cewar, duk da sun fito ne daga jam’iyyar adawa wanda hakan ke haifar masu da cikas wajan tabbatar da yaki da wasu manufofi da zasu zama illa a yankin Arewa, hakan baya sasu kasa a gwuiwa domin tabbatar da gabatar da kudinrin da zai bunkasa yankin arewa tare da samar da Cigaban al’ummar yankin.

Leave a Comment