Siyasa

Daruruwan Yan Jam’iyar APC Sun Koma NNPP a Bagwai

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shua’aibu Sani Bagwai

 

Daruruwan ‘yan Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar zuwa NNPP a garuruwan Badungu da Umbawa dake mazabar Sare-Sare a Karamar Hukumar Bagwai Jihar Kano.

Jagoran wadanda suka fice daga APCn Ado Muhd Badungu ya ce sun fice daga Jam’iyyar ce sakamakon rashin tabuga wani abun Kirki na ayyukan inganta rayuwar al’uma a yankunan na tsawon shekaru 8 da Jam’iyyar ke mulki.

Ya ce shekaru 8 babu komai ta bangaren cigaban ilmi da lafiya da ruwan Sha da hanyoyin mota da kuma takin zamani sai karya iri-iri ga kuma tsadar rayuwa ta addabi mutane.

Jagoran ya kara da cewa za su tabbatar da ganin cewa Jam’iyyar NNPP ta sami gagarumar nasara tun daga Kasa har sama a lokutan zabe musamman idan aka yi la’akari da gudunmowar da Sanata RMK ya bayar wajen cigaban rayuwar al’uma.

Da yake jawabin karbar ‘yan Jam’iyyar, Dantakarar Majalisar tarayya na Bagwai da Shanono kuma tsohon Kwamishina, Hon. Musa Sulaiman Shanono, ya tabbatar musu da cewa Jam’iyyar NNPP Jam’iyya ce da aka kafa ta domin Ceton al’uma daga matsanancin halin da Jam’iyyar APC ta jefa Kasar nan cikin shekaru 8.

Ku Karanta: Kiru-Bebeji: Zamu Tabbatar NNPP Ta Yi Nasara A Dukkan Matakai — Abdulmumin Kofa

Ya ce babu shakka daga dafifin mutanen da suka fito domin tarbar ayarinsu musamman Mata da matasa Jam’iyyar NNPP ce zata sami gagarumin rinjaye a zabukan da za a gudanar cikin yardar Allah.

Hon. Musa Sulaiman Shanono, ya tabbatar musu da cewa idan Jam’iyyar NNPP ta kafa gwamnati za su ga sauye-sauye na cigaba kamar dai yadda aka yi a gwamnatin Sanata RMK a baya.

Shi ma a jawabinsa, Dantakarar Majalisar Dokokin Jihar na Shanono da Bagwai, Hon. Ahmad Musa Bagwai, ya godewa mutanen yakin bisa gagarumin goyon bayan da suke baiwa Jam’iyyar wajen samun nasararta a zabukan da ke take, Sannan ya yi alwashin cewa za su kawowa al’umar yankin dauki ta fuskoki daban daban da zarar Jam’iyyar ta kafa gwamnati musamman idan aka yi la’akari da cewa dukkan al’umar yankin manoma ne.

Taron dai ya sami halartar jiga-jigan Jam’iyyar NNPP da ke Kananan Hukumomin Bagwai da Shanono.

Leave a Comment