Kasuwanci

Dalilaina Na Neman Takarar Shugabancin Kasuwar Wayoyin Hannu Ta Bata – Bashir

Written by Pyramid FM Kano

Daga: IBRAHIM SANI GAMA

Dan takarar shugabancin kungiyar Kasuwar masu hada-hadar wayoyin hannu ta kasuwar Bata ne ya sha wannan alwashin na kawo managartan shirye-shirye da zarar ya samu darewa kujerar shugabancin kungiyar kasuwar.

Bashir Hamza Baballe ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake yakin neman zabe a kasuwar dake Bata a nan Kano.

Bashir Hamza yace, daga cikin ci gaban da zai kawowa al’ummar kasuwar, akwai samar da tsaro da ingantaccen hasken wutar lantarki da samar da kyakykyawar alaka tsakanin ‘Yan kasuwa da abokanan cinikayyarsu na yau da kullum.

Dan takarar ya bayyana cewa, akwai tsarin da shugabancinsu yake da aniyar yi na shiga wajen Gwamnati da Bankunan Kasuwanci domin nemowa ‘yan kasuwar aron kudaden da babu kudin ruwa a cikinsu, wanda zai taimaka musu wajen bunkasa harkokin kasuwancinsu.

Bashir Hamza ya kara da cewa, akwai hanyoyin da ya tanada wajen magance matsalolin da ‘yan kasuwa ke fuskanta a bangaren biyan kudin hayar shaguna da bangaren biyan kudaden haraji.

Haka zalika, ta bangaren Gwamnati, shugabancin kungiyar kasuwar, zai yi ayyuka kafada da kafada wajen ciyar da al’ummar kasuwar masu hada-hadar wayoyin hannu gaba.

Daga karshe ya shawarci ‘Yan kasuwa da su bashi goyan bayan da suka kamata domin samun nasara a zaben da za’a gudanar a kasuwar, inda yace, da zarar sun samu damar lashe zabukan zai basu damar cika alkawuran da suka dauka.

Leave a Comment