Muhalli

Cushe Magudanan Ruwa Ke Jawo Ambaliya — Dan-azumi Gwarzo

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Sani Abdullahi Danbala Gwarzo

Sabon kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Kano ya bukaci al’ummar jihar Kano da su guji zuba shara a Magudanan ruwa domin hakan ke janyo Ambaliyar ruwa da ka iya sanadiyar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Alhaji Ibrahim Dan-azumi Gwarzo ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a ofishin sa.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamna Dakta Abdullahi Ganduje na Iya kokarin ta wajen samar da ayyukan cigaba ga al’umma.

Ku karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

Dan-azumi Gwarzo ya jajantawa daukacin Yan kasuwa a nan Kano da iftilain ambaliyar ruwan ya shafa da Kuma Mika taaziya ga iyalan wadanda suka rasu a rushewar ginin Nan Mai hawa biyu na kasuwar waya dake Kan titin Beirut.

Leave a Comment