Labaran Jiha

Cikin Watanni 8 Al’ummar Yannkin Bauchi Ta Kudu Sun Gamsu Da Wakilcinmu – Sanata Buba

Written by Admin

By: KABIR GETSO

Sanatan mai wakiltar yankin Bauchi ta Kudu Sanata Shehu Buba Umar ya bayyanna cewar tuni al’ummar yankinsa suka gamsu da wakilcinsa a kasa da watanni 8 da zabarsa domin ya wakilci yankin Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Sanatan ya bayyanna hakan ne a ganawa da wakilin Radio Nigeria Pyramid Kano a gidansa dake cikin garin Bauchi yace, tun a watan farko ya fara cika alkawarukan da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

Daga cikin ayyukan da ya fara, sun hada da samar da katafariyar makarantar horar da jami’an yaki da fasa kwauri ta kasa a yankin nasa, sannan bada jimawa ba ya samarwa matasa da dama ayyukan yi a matakin Gwamnatin Tarayya, sannan ya bijiro da tsarin Tallafawa Mata da matasa da tallafin Jari don suyi sana’o’i don dogara da kansu.

“Wani abun da ke farantawa al’ummar yankin shine, yadda ya ware kowanne karshen wata domin baro Abuja yazo yankin nasa domin ganawa da mutanen nasa wanda hakan wani sabon abu ne da al’ummar yankin basu saba ganin hakan ba,” Inji shi.

Sanata Shehu Buba ya kara da cewar, akwai kuduri masu matukar mahimmanci da ya gabatar a majalisa wanda da zarar ya tsallake to babu shakka al’ummar yankin nasa dama Jihar Bauchi zasu dara matuka. Bangaren Ilimi ma, Sanatan yayi kyakkyawan tsari domin bunkasa sha’anin ilimin tun daga matakin firamare har zuwa na gaba da sakandire don tallafawa al’ummar yankin nasa.

Sanatan ya yabawa daukacin al’ummar jihar Bauchi musamman na yankin Bauchi ta kudu bisa irin kwarin Gwuiwa da goyon da suke bashi don cigaba da bijiro kyawawan ayyukan da zai amfanesu.

Yace, duk da shi kadai ne mai babbar Kujera daga jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, amma hakan bai hana shi kula da ‘yan jam’iyyar ba domin tallafa masu a koda yaushe don rage radadin rayuwar da ake ciki, sannan ya shawarce su da su cigaba da bashi goyon baya domin nan bada dadewa ba al’umma zasu kara fahimtar irin kyakkyawan tanadin da akai masu.

Leave a Comment