Labaran Kasa Manyan Labarai

CBN ya dauki matakin tabbatar da samun sabbin takardun Naira

Written by Pyramid FM Kano

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce yana kokarin magance kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta na samun sabbin takardun kudi na Naira.

 

Gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Legas.

 

Mista Emefiele ya ce babban bankin na sane da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki, ya kuma yi alkawarin zage damtse wajen magance matsalolin.

 

Gwamnan babban bankin na CBN ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, ana kokarin kara yin musanya da kudade ga bankunan masu karamin karfi da kuma daukar manyan jami’ai 30,000 a kasashen da ke bayan fage domin a hanzarta yada sabbin takardun kudi na Naira.

 

Babban bankin na CBN yana hada hannu da bankunan domin samar da wasu tashoshi masu sauki ga ‘yan Najeriya, in ji shi.

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su ba shi kwanaki bakwai domin magance kalubalen da suke fuskanta a yayin da suke kokarin samun sabbin takardun kudi na Naira.

Leave a Comment