Kasuwanci

Canjin Kudi: Muna Rokon Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Tsarinta — Direbobin Akori-kura

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Kungiyar matuka motar Akori kura ta kasa reshen jihar Kano dake Railway ta koka kan yadda yayanta ke fuskantar kalubale sakamakon dokar mayar da tsoffin kudade ga bankuna kafin nan da karshen watan nan.

Shugaban kungiyar Alhaji Dan Iya Bala ne ya yi wannan koken a zantawarta da manema labarai a ofishinsa.

Dan Iya Bala ya bayyana cewar tsarin ya saka ‘Ya’yan kungiyar cikin matsaloli kasancewar suna daukar kayayyaki daga nan kano zuwa sassa daban daban na kasar nan, amma Canjin Kudin ya janyo mutane a wasu Jihohin basa Karbar tsofaffun Kudade.

Don haka Shugaban ya umarci yayan kungiyar cewar duk wanda bashi da asusun ajiya banki ya tabbatar ya mallakeshi.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Gwamnatoci Don Bukasa Kasuwancin mu — Shugaban Kasuwar Gyada

Shugaban ya kuma bayyana cewar idan har gwamnati ta ce zata yi wani abu to lallai yana da muhimmanci don haka yake kira ga yayan kungiyarsu kan cewar su zauna cikin shiri Wato duk wanda yasan asusun ajiyarsa na banki na da matsala yaje ya gyara nan da kafin lokacin rufe karbar tsoffin kudade da babban bankin kasar nan ya sanya.

Dan Iya Bala ya kuma yi Kira ga gwamnatin tarayya kan ta daure ta kara waadin lokacin daina yin amfani da tsoffin kudaden da ta sanya kasancewar Yan Nigeria musamman mazauna karkara na kokawa da cewar tsarin zai haifar wa da tsarin kasuwacinsu barazana sakamakon mafi akasarin su basu da asusun ajiyar banki.

Ku Karanta: Mun Shirya Ceto Kano, Inganta Kasuwanci Da Gina Al’umma Idan Mukayi Nasarar Cin Zabe — Tanko Yakasai

Daga nan shugaban kungiyar ya shawarci yan kungiyar da su kasance masu bin doka da oda a dukkan lamuran su kuma su rungumi dukkan wani tsari da gwamnati ta bijiro dashi don cigaban kasa da bunkasar tattalin arzikin kasar nan da harkokin kasuwanci da kuma sana’o’i.

Leave a Comment