Kasuwanci

Burinmu na samawa matasa aikin yi, shi ke kara habbaka Kamfaninmu – Nasar

By: KABIR GETSO

A kokarin Kamfanin Yusra Yogurt na saukaka wa kwastomominsa wuraren sayen fura da nono, samar da aiyukan yi ga matasa, inganta sana’ar fura da nono da kuma kawo wa kasa ci gaba, ya sake bude sabon shagonsa a kan titin Tsohuwar Jami’ar Bayero, dake Unguwar Kabuga.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban kamfanin, Nasar Kabiru Waya inda yace wannan shine shagon su na goma a Jihar Kano, kuma suna da shirin bude wasu a sassa na jihohin kasar nan, da kuma wadanda aka riga aka bude a Sakkwato da Suleja.

Nasar ya kara da cewa Yusra Yoghurt na sayar da 330ml da 550ml da kuma 1ltr, yace kuma suna da wasu kudure kudure na yin abubuwa da yawa Kamar ruwa, ice scream Biredi da dai sauran su.

Shugaban yace duk da tsadar kayayyaki a kasuwanni hakan bai sa sun rage ingancin kayayyakin su ba, sai dai karawa da suke yi.

Ya kuma yi kira ga mutanen da suke son shigowa domin hadaka a kasuwancin da su zo kofar su a bude take.

A nasa jawabin Muhammad Murtala ya ce sun bude wannan kamfani ne domin samawa Jihar Kano kudin shiga da kuma samar da aiyukan yi ga matasa sabo da ci gaban kasa baki daya.

Muhammad ya kara da nuna jin dadin sa da karbuwar da suka yi, yana mai cewa abokan cinikaiyar su na yabawa da kuma nuna gamsuwar su da Yusra Yoghurt.

Yace suna da kwararrun ma’aikata tare da injina na sarrarafa fura da nono masu in ganci, kuma sai da kamfanin Yusra Yoghurt ya sami sahalewar hukumar NAFDAC kafin ya fara gudanar da harkokin sa.

Leave a Comment