Yanzu-Yanzu

Batanci ga Annabi: Darikar Tijjaniyya ta yi Allah wadai – Sheik Khalifa Maihula

By: MUKHTAR YAHAYA SHEHU

 

Majalisar Shura ta darikar Tijjaniyya tayi kira ga Jami’an tsaro da sauran dukkan masu ruwa da tsaki dake jihar nan su dauki matakin gaggawa kan hukunta wadanda sukeyin kalaman batanci ko nuna rashin ladabi ga Annabi Muhammadu SAW.

Wannan kira yana kunshe ne cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Abubakar Balarabe Kofar Na’isa a madadin Sakataren Majalisar Shura Barista Habibu Dan Almajiri ya fitar a madadin Shugaban Majalisar Khalifa Sheikh Sani Shehu Maihula.

Yace Gwamnati da hukumomin tsaro shine matakin farko da ya kamata abi wajan kamo wadanda sukeyin munanan kalamai na rashin ladabi ga janibin Annabi Muhammadu SAW.

Barista Dan Almajiri yace abin takaici ne da bakin ciki a gari irin Kano garin da ya amsa sunansa wajan yin biyayya da soyayyar Annabi Muhammadu ace wasu mutane suna bayyana munanan kalamai da nuna rashin ladabi ga fiyayyen halitta.

Ya karanto ayoyin alqur’ani mai tsarki da Hadisai da suke tabbatar da yin ladafi da biyayya ga Annabi Muhammadu SAW musamman wadanda sukayi magana akan ladduban yin furuci ga Annabi Muhammadu SAW.

Leave a Comment