Addini

Barau Maliya Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Zagayowar Maulidin Annabi SAW

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Yayin da al’ummar Musulmi a Najeriya suka bi sahun sauran kasashen duniya wajen gudanar da bukukuwan Maulidin fiyayyen halitta Manzon Allah S.A.W. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi kira ga ‘yan uwa musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen kara karfafa koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammad (SAW).

Sanata Barau, a cikin sakon murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya bayyana cewa, hakika Manzon Allah SAW babban abin koyi ne ga kowa da kowa.

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba 27 ga watan Satumbar shekarar 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

“Yayin da muke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabinmu Muhammadu (SAW), mu yi nazari a kan kyawawan dabi’unsa da koyarwarsa, mu kuma yi koyi da shi a cikin al’amuran mu na yau da kullum. Mu yi koyi da darussan tausayi, zaman lafiya da taimakon juna kamar yadda Annabinmu mai daraja ya yi umarni,” inji shi.

Ya kuma nanata kudurin majalisar na tafiya akan tsarin da zai tallafa wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin ya cika alkawuran da yayi na cigaba a yayin yakin neman zabensa.

Ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya, inda ya ba su tabbacin cewa manufofin da shugaba Tinubu ke tsarawa za su magance matsalolin da ke addabar al’umma.

Leave a Comment