Kasuwanci

Bamu Ji Dadin Tsarin Takaita Cire Kudin Da CBN Ya Kawo Ba — Kungiyar Masu Safarar Dabbobin

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Shehu Sulaiman Sharfadi

Kungiyar masu fataucin shanu da dabbobi ta kasa ta koka dangane da kaidojin da babban bankin Nigeria CBN ya samar na takaita yawan kudaden da zaa fitar a bankuna ba, yana Mai cewar hakan zai durkusar da kasuwancin yayanta.

Shugaban kungiyar Alhaji Mustafa Ali ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan Kano.

Acewar Mustafa Ali kamata yayi gwamnatin tarayya ta Samar da tsarin da zai ceci yan kasuwa musamman kanana kafin ta aiwatar da sabon tsarin na sauya fasalin kudi ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin kasuwanci a kasar nan.

Ya kuma koka dangane da yadda tsarin kasuwacinsu zai fuskanci kalubale idan har bankin na CBN ya dage akan sabbin kaidoji da ya bijiro dasu kan cewar mutum daya ba zai cire kudin daya haura naira dubu dari ba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba.

Ku Karanta: Kamfanin Galaxy Backbone na bajekolin ayyukansa A babban taron cibiyar sadarwa ta Kasa

Shugaban ya bayyana cewar kasar nan ba ta Kai munzalin da za tayi amfani da wannan sabon tsarin da ake yiwa lakabi da cashless policy ba kasancewar tsarin tattalin arzikin kasar na cikin mashashshara.

Ku Karanta: Ku Kyauta Rayuwar Al’umma Da Kudaden Shigar Ku, Aminu Ado Ga Gwamnatoci

Don Haka yake kira ga gwamnatin tarayya kan ta gaggauta yin duba na tsanaki kan wannan sabon tsarin da ba zai haifar wa da kasarnan da mai ido ba wanda idan gwamnati bata farga ba zai lalata kasuwancin dubunnan alumma a fadin kasar nan.

Daga karshe yayi kira ga yayan kungiyarsu kan cewar su cigaba da baiwa Shugabancin kungiyar hadin kai da goyon baya kasancewar kungiyar a shirye take wajen kare musu mutuncinsu da kuma kwatar musu yancinsu musamman wadanda ke gudanar da kasuwacinsu a sassa daban daban na jihohin kudancin kasarnan.

Leave a Comment