Manyan Labarai

Ba Zan Fasa Hidimtawa Al’ummar jihar Kano Ba – Tsoho Shugaban Kungiyar NURTW ta Kano Alh. Abdullahi

Written by Admin

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyoyin direbobin motocin haya da dama a jihar Kano, sun bayyana rashin jin dadinsu bisa kin sanya sunan Alh. Abdullahi Isah daga cikin jagororin da aka kaddamar karkashin ma’aikatar sufuri na kungiyar NURTW ta jihar Kano domin shugabantar kungiyar ta jihar Kano.

Sakataren kungiyar NURTW Bus 9 Malam Kato Alh. Garba ne ya bayyana haka a wata zantawa da manema labarai anan Kano.

Yace, kwamishinan harkokin sufuri na jihar Kano, Hon. Muhammad Ibrahim Diggol ya kamata yayi duba na musamman domin neman hanyoyin magance matsalolin dake kunshe a cikin kungiyar NURTW ta kasa reshen jihar Kano.

Sakataren ya kara da cewa, akwai kungiyoyin sufuri da wanda da ba ma na sufuri ba’a jihar Kano, musamman na kananan hukumomi sun amfana da yawa akan taimakon da Alh. Abdullahi Isah yake bayarwa, amma, abun mamaki kwamishinan harkokin sufuri na jihar Kano, Muhammad Ibrahim Diggol yayi Kitso da Kwarkwata cikin Shugabannin da aka rantsar helkwatar kungiyar NURTW ta jihar Kano.

Wata kungiyar matasan direbobi ta kananan hukumomi 44 a nan jihar Kano, ta yi mutukar nuna damuwarta dangane da cushen da ake zargin an yi cikin kunshi shugabancin da ma’aikatar ta sufuri tayi, wanda hakan yakan fitar da wasu ‘Ya’yan jam’iyya daga cikin jamiyya da kungiyoyin dake hidimtawa al’ummar jihar Kano.

To, sai dai kuma, idon Gwamnatin jihar Kano da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin kungiyoyin sufuri, basu dauki matakai ba, wasu daga cikin ‘yan jam’iyyun za su rika ficewa daga jam’iyya, musamman ta NNPP dake mulki a jihar Kano kamar yadda kungiyar matasan direbobi ta bayyana a cikin wata takardar shawara da ta aikewa kwamishinan harkokin sufuri domin neman duba akan lamarin.

Sai dai mun tuntubi wanda aka cire daga cikin jagororin kungiyar NURTW ta kasa reshen jihar Kano, wanda kuma, mataimakin shugaba ne a kungiyar NURTW Bus 9 dake Tashar Malam Kato Alh. Abdullahi Isah, dangane da wannan lamari na kungiyar NURTW ta jihar Kano, inda yace, ya godewa Allah Subhanahu Wata’ala da ya bashi damar hidimtawa al’ummar jihar Kano a cikin tsawon lokacin da ya rike mukamin ma’ajin kungiyar NURTW da yadda al’ummar jihar Kano suke ta yaba masa bisa gudunmawa da yake bayarwa ga direbobi tun daga kananan hukumomi zuwa jiha da sauran makwaftan jihohi na Kudu, Arewa, Gabas da kuma Yamma akan duk abubuwan da suka taso.

Sai muka tambayesh akan batun makudan kudaden daya kashewa Gwamnati mai ci da Kungiyoyi a lokacin yakin neman zaben kafa Gwamnati da kungiyoyin harkokin sufuri domin ganin sun tsaya da kafafuwansu.

Abdullahi Isah ya bayyana cewa, ba wai yayi hakan domin neman wasu abubuwa ba, sai don hidimtawa alummar Najeriya musamman na jihar Kano, wajen ganin jihar ta kara bunkasa ta fannin harkokin sufuri da kasuwanci da tattalin arziki, inda ya jaddada cewar, don an fitar da shi daga cikin jagororin kungiyar NURTW ta kasa reshen jihar Kano, ba zai fasa taimakawa al’ummar jihar Kano ba, domin jihar Kano ita ce a zuciyarsa.

Daga karshe Abdullahi Isah, ya shawarci gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, daya kara sanya idanu a fannin harkokin kungiyoyin sufuri baki daya domin samarwa matasan direbobi na jihar Kano sana’o’in dogaro da kai, da ma yin gogayya da sauran jihohin kasar nan.

Leave a Comment