Da Dumi-Dumi

Ba Zamu Saurara Ba Wajen Yaƙi Da Cin Zarafin ‘ya’ya Mata A Fadin Jihar Kano

Written by Admin

Daga: KABIR GETSO

Shugabar kungiyar Hajiya Gambo Abdullahi ta bayyana hakan ne yayin wani taron Yaqi da cin zarafin ‘ya’ya mata da Yara kanana a Kano. – Kungiyar yaki da cin zarafin mata

” Cin zarafin ‘ya’ya mata na kara yawa a kano don haka dole mu tashi tsaye don ganin mun yaki wannan harkar, don haka muna bukatar hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki don ganin mun kau da wannan mummunar dabi’ar a cikin al’ummar mu”. A cewar Hajiya Gambo

Ina baiwa iyaye shawarar su kara zage dantse wajen ganin sun kyautata rayuwar ya’yansu, musamman ma masu tura ya’yan su aikatau, saboda ana azabtar da su kuma hakan cin zarafi ne, ya kamata iyaye su sani cewa hukuma ba zata saurarawa duk wanda aka kama da cin zarafin ‘ya’ya mata ko kananan yara”.

Ta kuma qara da cewa “samari masu yaudarar yara mata da abun hannun su shi ma cin zarafi ne, wani lokacin ma a cikin gida ake bata yaran kuma zamu dauki dukkanin matakan da suka dace wajen tabbatar da an hukunta duk wanda aka kama da hannu wajen lalata rayuwar yara”.

Ta kuma tabbatar da cewar Kungiyar su ba zata zuba Ido tana kallon wannan mummunar dabi’a ta bata ya’ya mata na kara ta’azzara a cikin al’umma ba.

Dr. Hajiya Hadiza Gishiri wace Uwace A wannan Qunqiyar tana kira ga VC iyaye Mata da suji tsoron Allah su kula da yayansu musamman masu kai ya’yan su aikatau Inda ta ce ” suma fa ya’ya ne kamar kowa” ta Kuma yi addu’a Allah ya Basu sa’a a Wannan tafiyar tasu.

Taron dai Yasami Halartar Gungiyoyin Mata daban daban Da kuma Maza Da Yan Jaridu Ciki Harda Tsofafin Sojoji.

Leave a Comment