Ilimi

ASUP Tayi sabbin Shugabanni a Husaini Adamu Polytechnic Kazaure

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar malaman kwalejin fasaha ta Usaini Adamu dake Kazaure a jihar Jigawa wato (Hussain Adamu Federal Polytechnic, Kazaure) ta zabi Sabbin Shugabannin ta.

Zaben wanda ya gudana a harabar Kwalejin, an gudanar da shi bisa kyakkyawan tsari da tanadi.

Dakta Abdul’aziz Ibarhaim Gwadabe wanda ya lashe zaben a matsayin Shugaba ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa samun nasarar tare da shan alwashin aiki kafada kafada da saura Shugabanni domin ciyar da kungiyar gaba.

Ya kara da cewa nasarar ba tasa bace shi kadai nasara ce da ta shafi dukkanin ‘ya’yan Kungiyar, Musamman la’akari da cewar tun a baya an samu nasarori da dama.

Ku Karanta: Muna Bukatar Tallafin Iyaye, Dattawa da Gwamnatin Don Gina Matsuguni na Din-Din-Din — Shugaban B. I. T.

Dakta Abdul’aziz Ibarhaim Gwadabe ya ce nasarar wacce ya samu a matsayin ta karo na biyu alama ce dake nuna mutane sun Gamsu da ayyukan da kungiyar take gudanarwa karkashin jagorancin sa, kuma zai cigaba da jajircewa da aiki tukuru da ‘ya’yan kungiyar domin bashi damar cigaba da ayyuka da nufin ciyar da kungiyar gaba.

Daga cikin nasarori da suka samu a baya sun hada da kulla kyakkyawan Alaka da samar da Gidauniya ta Musamman don kyautata rayuwar malaman Kwalejin da kuma hadai kai da sauran hukumomi irin su NITDA don samun horo na Musamman don kyautata tsarin aiki

Dakta Abdul’aziz yayi kira ga wadanda basu samu nasarar ba da su hada kai domin cigaba da samun nasara yadda ya kamata.

Leave a Comment