Siyasa

APC Zata Lashe Zabe a Kano Kafin 12 Rana — Faizu Alfindiki

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kamal Yakubu Ali

A shirye shiryen da jamiyyar Apc ke gudanarwa na ganin ta samu Nasara a zaben shekarar 2023 shugaban karamar hukumar birni da kewaye Honourable Faizu Alfindiki, ya jagoranci taro na musamman na mata zallah wadanda suka fito daga unguwar marmara.

Ya ce kafin karfe goma Sha biyu (12:00pm) na ranar zaben za’a tabbatar jam’iyar APC ta yi Nasara a Kano.

Kwamared Faizu Alfindiki wanda shi ne shugaban kwamitin matasa na yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya bayyana cewar APC ta shirya tsaf domin fafatawa da kowacce Jam’iyya la’akari da ingantattun yan takara da aka fito da su, yana mai cewar Dan takarar da Jam’iyyar su ta APC ta tsayar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya kasance mafi cancanta a cikin ‘yan takarar gwamna a jihar Kano.

Ku Karanta: Zaben 2023: Ku Zabi Shugabanni Na Gari Kamar Gawuna — Tanko Yakasai

Alfindiki ya bayyana cewa zaben Gawuna da Mataimakin sa Murtala Sule Garo zasu sake mayar da Jihar kan turbar ci gaba da inganta rayuwar al’umma, inda ya baiwa mata da suka halarci taron kyautar dubu 200 ya kuma rabawa marayu kayan karatu a yayin taron.

Shima Dan Majalisar Dokokinb Jihar Kano na karamar hukumar birni Maje Ahmad Gwangwazo, da kuma kakin yakin naiman zaben “Gawuna Garo Kano State”, Kwamared Mohammed Garba  sun yi kira ga magoya bayansu da su zabi  APC a 2023.

Ku Karanta: Ina Neman Afuwar Duk Wanda Na Batawa — Hafizu Kawu

Malam Mohammed Garba a yayin taron ya bada kyautar Naira dubu 200 ga mata, yayin da maza suma aka basu Naira dubu 200 domin samar da ayyukanyi da ababen More rayuwa.

Leave a Comment