Da Dumi-Dumi

Angudanar Da Taron Addu’a Ga Falasdinawa

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Saminu Ibrahim Magashi.

Gangamin taron addu’ar ya gudana ne a unguwar Sharifai dake jihar Kano akarkashin Mu’assasasul Imam Abdulkarim Almaghili wadda Sharif Abdulkarim Salihu Almaghili yake jagoranta.

Inda ya bayyana cewa, sun shirya wannan taro ne saboda basu da damar zuwa kafa da kafa domin bawa musulman dake cikin wanann ibtila’i gudunmawar kayan yaki hakance tasa suka gabatar da addu’a domin wanzuwar zaman lafiya a yankin.

A karshe yayi kira da al’ummar musulmin duniya dasu dinga saka Falasdinawan a duk addu’o’insu na yau da kullum.

Wasu daga cikin mahalatta taron daga sassan garuruwan Najeriya sun bayyana dalilin zuwan su Kano domin muhimmancin wannan addu’a.

Taron dai yasamu halartar Sharifai daga gurare da dama a fadin Najeriya.

Leave a Comment