Addini

An Shiryawa ‘Yan Jaridu Mata Lacca Domin Watan Ramadan

Written by Admin

Daga: Jamila Suleiman Aliyu

Kungiyar ‘yan jaridu mata ta kasa, ta shirya taron fadakarwa ga mata ‘yan jaridu a jihar Kano. Sakatariyar kungiyar ta kasa Hajiya Wasila Ladan ita ta jagoranchi taron wanda ta bayyana shi a matsayin irinshi na farko a tarihin kafuwar kungiyar shekaru talatin baya.

An yayin gabatar da laccocin ga mata ‘yan jaridun an ja hankalinsu akan roman da ake samu a watan na Ramadan tare da jan hankalin mata domin rabauta dan samun falalar da ke goman karshen watan domin a hadu a tsira. Malaman da sukayi fadakarwa sun hadar da Malama Sa’adatu Ali Ahmed wacce tayi jan hankali da alkhairin da yake tattare da shi yayin sahur da kuma Sheik Abdurkahir Jurjaniy Awwal Kabara wanda yayi jan hakali akan ayyukan alkhairi a watan. Shugabannin gidajen rediyo da talabijin da kuma babban sakatare a ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano na daga cikin mahalatta taron.

Wakiliyarmu, Jamila Sulaiman Aliyu ta bamu rahoton cewa a yayin gudanar da lakcar an mika kayan masarufi ga wasu daga cikin mahalatta taron.

Leave a Comment