Labaran Kasa

An Rantsar da Barista Rabi’u Rijiyar Lemo a Matsayin Babban Alkalin Yankin Abuja

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Hukumar shari’a ta Babban birnin tarayya Abuja ta gudanar da taron nadin alkalai 12 wadanda da aka dauka daga jihohin kasar nan a matsayin Manyan Alkalan yanki a Abuja.

Toron dai ya gudana a karkashin jagorancin Grand khadi Hon Ibrahim Imam.

Cikin wadanda aka rantsar din sun hadar da barrister Rabiu Sa’id Rijiyar Lemo wanda aka rantsar da shi a matsayin Babban Alkalin Yanki na Babban birnin tarayyar.

Ku Karanta: Kisan Ummulkhulsum Sani: Za’a Gurfanar da Geng Quarong a Kotu a 4 ga Oktoban 2022

Barrista Rabiu Sa’id Rijiyar lemo ya yana wakiltar jihar Kano cikin wadanda aka nada.

Jim kadan bayan kammala nadin ya yiwa Allah godiya, ya kuma roki al’umma da su taya shi addu’ar sauke nauyin da ya dauka.

Leave a Comment