Da Dumi-Dumi

An kawo karshen Zadar Aure A Garin Bidir fake Jihar Bauchi

Written by Admin

By: KABIR GETSO

A Garin Bidir kasar Hakimin Madara karamar hukumar Katagum Jihar Bauchi.

Sakamakon zaman kawo daidaito da fahimtar juna mutanen Garin Bidir sun kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Habibu Abdulkarim Bidir domin jagorantar kawo sauki a cikin Al’alar Aure da ke haddasa kasa wahalar aure

Jami’in hukumar shari’ar musulunci ta jihar Bauchi dake shiyyar Katagum Mal.Ridwan Moh’d Khairan ya jagoranci kaddamar da wannan kyautata aure a kasar Bidir, Mal. Khairan ya kara da jan hankalin Sarkin da ya dage ya hana masu zuwa bikin ajo da garaya garin domin fata tarbiyyar ” yayan mutane da sukeyi.

A yayin gabatar da taron a ranar Asabatr din da ta gabata daukacin zawarawan da magidanta da matasa sun halarci wajen da gamin da Alwashin dorewar hakan, taron da ya gudana a fadar sarkin bidir.

Cikin jawabinsa Hakimin Bifir Alhaji Baffa Moh’d ya godewa mahalarta taron da kwamitin shirya taron na garirin Bidir da hukumar shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi , sarkin na Bidir ya gargadin matasan da ” yammata da iyayensu da kada su kaucewa wannan dokar domin a rage aikata fasadi a rika samun damar yin auren.

Rahoto Daga Musa Usman Sautussunnah Azare.

Leave a Comment