Labaran Jiha

An karrama Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Sani Abdullahi Dan-Bala Gwarzo.

Iyaye da Masu ruwa da tsaki a kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa reshan jihar Kano sun karrama shugaban kungiyar Kwamaret Abdullahi Muhammad Gwarzo.

Sun karrama shi ne dogaro da tarihin da ya kafa sakamakon ayyukan cigaban kungiyar ta ba’a taba yin irin sa ba.

Masu ruwa da tsakin sunyi fatan zai cigaba da gudanar da ayyukan cigaban kungiyar da ‘ya’yan ta da nufin kawo sauyi Mai ma’ana.

Ku karanta: An Hallaka Barawon Babura da Ya Addabi Yankin Gwarzo da Dayi

A nasa bangaren, Kwamared Abdullahi Gwarzo wanda kuma shine Matawallen Gwarzo ya bayyana godiyarsa ga daukacin al’ummar dasu ka halarci taron ciki harda kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Lamin Sani Zawuya da Shugaban karamar Hukumar Birnin da Kewaye Fa’izu Alfindiki da Shugaban Kungiyar shuwagabannin kananan hukumomi na jihar Kano, Baffa Takai da sauran wasu da dama.

Kwamaret Gwarzo ya kuma bada tabbacin dorawa daga inda ya tsaya da nufin cigaban al’umma.

Leave a Comment