Labaran Jiha

An Hallaka Barawon Babura da Ya Addabi Yankin Gwarzo da Dayi

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kabiru Muhammad Getso

Wasu Mutane da ba’a San ko suwaye ba sun halaka wani mutum da yayi kaurin suna wajen satar Babura masu kafa biyu a yankin Karamar Gwarzo dake jihar Kano da yankin Dayi a jihar Katsina.

Barawon kafin rasuwarsa yayi yunkurin karbe babur din wani mutum a wata hanya kusa da garin kwantara inda ya buge mai babur din kuma ya karbe shi ya Kuma bar shi nan a kwance.

Saidai bayan da shi mai babur din ya samu nisawa sai ya kira waya ga wasu a can gaba inda suka tare shi, kuma suka sassarashi har ya rasu.

Barawon Magidanci mai kimanin Shekaru 50, an same shi da wata hoda mai bugar da mutane da kuma wasu kudade, Kuma tuni aka garzaya da shi Sashin adana gawawwaki dake Babban Asibitin Gwarzo.

Ku karanta: Ganduje Ya tura Sunan Ali Burum-Burum Majalisa don Nada shi Kwamishina

Mun tuntunbi Jam’in Hulda da Jama’a na rundunan yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa wanda ya ce da zarar ya gama bibiyar lamarin zai yi karin bayani.

Leave a Comment