Da Dumi-Dumi

An Fara Bikin Auren Zawarawa a Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILA SULEIMAN ALIYU

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da auren gata na maza da mata dubu daya da dari takwas a ranar juma’a.

Babban Daraktan hukumar Malam Abba Sa’idu Sufi shine ya bayyana hakan ga manema labarai ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Lawan Ibrahim Fagge.

Ya ce, a yau hukumar ta karbi bakuncin waliyan bangarorin biyu angwaye da amare a shelkwatar hukumar domin gabatar da siga ta karbar auren da kuma bayarwa a bangare guda.

Malam Lawan ya ce waliyan suna yin sigar nema data bayarwa a masallacin hukumar a inda wakilan hukumar suke shaidawa.

Ya ce, hukumar bayan an daura auren zata jagoranci shagalin bukin wanda zai hadar da raye raye da tande tande da lashe lashe biyo bayan daurin auren sannan kuma anbawa ko wane ango kudin sadakin dazai dankawa amaryarsa tare da bawa amaren jarin dubu ashirin ko wannensu domin ya zama tallafin sana’a.

Haka zalika, babban daraktan ya ce, abin a yabawa wata kungiya ta ABBA Gida Gida Mai koyawa mata sana’o’i wadda tayi alkawariin koyawa matasan sana’o’i kyauta domin dogaro da kansu.

Leave a Comment