Da Dumi-Dumi

An Bukaci Tsofaffin Daliban Makarantun Ilmi Maizurfi Dasu Kula Da Zumunci

Written by Admin

By: MUHAMMAD ADAMU ABUBAKAR 

An bukaci tsofaffin daliban makarantun ilmi maizurfi dasu kula da zumunci.

Shugaban kungiyar daliban da suka kammala Diploma a shekarar
2002, Dr. Tahir Abba Muwappaq ne ya bayyana hakan a yayin taron cikarsu shekara 21, da gama karatu.

Dr. Tahir yace riko da zumunci na da matukar muhimmanci a rayuwar al’umma inda ya shawarci abokan karatun nasa da su cigaba da girmama juna.

Daya Daliban, Rabiu Jibrin Idris yabawa gaya bisa damar halartar taron da aka yi.

A jawabansu daban daban Malaman da suka koyar da Daliban Farfesa Abubakar Salisu Garba da Ahmad Garba Tamburawa da kuma Ahmad Aminu Zanna yabawa dangane da shirya taron a wannan lokaci dama kira ga daliban da su zama tsintsiya madaurinki daya.

A jawabinta na godiya, Maryam Ibrahim Wada ga dukkanin wadanda suka halarci taron da wadanda suka bada gudunmawa domin samun nasararsa.

Leave a Comment