Labaran Jiha

An Bukaci Sabbin Shugabannin Cibiyar Hulda Da Jama’a Su Nuna Kwarewa A Aikinsu

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Mataimakin gwamnan Jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya taya sabon shugabancin cibiyar horas da harkokin hulda da jama’a ta Kasa reshen jihar Kano murna.

A cikin sanarwar da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan ya fitar Ibrahim Garba Shuaibu yace zaben sabbin shugabannin wanda ya gudana a ranar juma’a na daga cikin kokarin cibiyar wajen samar da kwararru a bangaren hulda da jama’a.

Gwarzo ya bayyana cewar zaben shugabannin an yi shi ne bisa cancanta da kwarewa wadanda zasu iya tafiyar da jagoranci a cibiyar.

Mataimakin gwamnan, ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga sabbin shugabannin wajen sanya kwarewa a cikin aikin su domin ciyar da cibiyar gaba.

Ya kuma bukacesu da suyi aiki da gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a bangaren domin ciyar da jihar nan gaba.

Daga cikin sabbin shugabannin akwai Aliyu Yusuf a matsayin shugaba, Ismail Ammani mai zare a matsayin mataimakin shugaba, Abdullahi D Abdullahi a matsayin ma’aji sai Usman Gwadabe a matsayin sakatare.

Sauran sun hadar da Muhammad Dahiru Idris a matsayin mataimakin sakatare, Samira Sulaiman a matsayin shugabar sashen hulda da jama’a, Abdullahi Abba Hassan a matsayin sakataren kudi da kuma Ado Sa’id Warawa a matsayin mai binciken kudi.

Leave a Comment