Ilimi Lafiya

Amosanin-Jini: Za Mu Tallafawa Masu Cutar Ta Kowacce Hanya — Sarkin Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama

Masarautar jihar Kano ta Sha alwashin tallafawa kungiyar masu larurar cutar amosanin jini da kuma wayar da kan alumma muhimmancin yin gwaji kafin aure domin kaucewa kamuwa da cututtuka daban-daban.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya bada tabbacin hakan a lokacin da kungiyar ta Kai masa ziyara da kuma bashi lambar girmamawa a fadarsa dake Kano.

Maimartaba Sarkin ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da shugabanni masu rike da masarautun gargajiya da hukumomin Lafiya da sauransu da su tabbatar da cewa sun baiwa kungiyar hadin kai wajen ganin ta wayar da kan alumma amfanin yin gwaji kafin aure.

Ado Bayero, ya bayyana farin cikinsa bisa jajircewar kungiyar da kuma yadda ya ga ‘ya’yan kungiyar duk matasa ne, yana mai cewar sune kashin bayan cigaban kowacce tafiya.

Sarkin ya kuma godewa Shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu Gizina, bisa jajircewar da gudunmawar da yake bayarwa wajen wayar da kan alumma muhimmancin yin gwaji kafin aure, inda kuma, ya yabawa kungiyar bisa karramawa da ta yi masa da bashi matsayin uban ta da nufin cigaban al’umma.

Ku karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

A jawabinsa tun da farko, shugaban kungiyar Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu Gizina, ya ce sun kaiwa Mai martaba Sarkin Ziyarar ne domin neman Masarautar ta tallafawa yunkurin kungiyar wajen ganin an baiwa dagatai da masu unguwanni umarnin tabbatar da an aiwatar da gwajin jini karfin Aure.

Maharazu Ibrahim ya ce kungiyar zata ci gaba da wayar da kan alumma yadda ya kamata a lungu da sako na birni da kankara da kananan hukumomi dake jihar nan Amfanin yin gwaji kafin aure.

Haka zalika, ya yabawa Mai martaba Sarkin bisa dama da ya baiwa kungiyar da shawarwarin da suka kamata musamman domin wayar da kan alumma musammancin yin gwaji kafin aure a jihar Kano.

Ya ce kuginyar za ta yi aiki da dukkan shawarwarin da Mai martaba sarkin ya basu domin samun nasara.

Leave a Comment