Yanzu-Yanzu

Al’umma su kula da bin ka’idojin kubuta daga annobar sankarau – Dr Bashir Bala Getso

 

By: Kabit Getso

Shugaban kwalejin kimiyyar tsabtar Muhalli ta Jihar Kano Dr Bashir Bala Getso ya bayyan annobar sankarau a matsayin babbar barazana ga lafiyar Al’umma.

Getso ya bayyanna hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa a inda yace, a waannan lokaci da ake dashi na dumamar yanayi wajibi ne da a tabbatar an bar tagogi a bude domin samun wadatuwar iska a dakunan kwanciya wanda hakan kan zama rigakafin kubuta daga cutar.

Cutar Sankarau cutace da ke yaduwa a lokaci irin wannan na zafi ta hanyar cuduwa da nunfashi da yanayin zubar da majina ko kaki da sauran wasu hanyoyi da kwayoyin cutar ke yaduwa.

kazalika cutar na da sauyin yaduwa da kuma hadarin gaske don haka ya zama wajibi da zarar anga alamominta a hanzarta ziyartar asibiti mafi kusa.

Daga cikin Alamomin cutar akwai zafin jiki, sarkewar nufashi wanda takanyi saurin illa ga kananan yara masu matsakaitan shekaru.

Dr. Bashir Getso ya yabawa Gwamnaatin Jihar Kano bisa kokarinta na yin duk mai yiwuwa wajen wayar da kan al’umma tare da bin duk matakan da ya kamata wajen magance yaduwar cutar.

Leave a Comment