Labaran Jiha Muhalli

Al’umma Na Rokon Gwamna Da Ya Kai Dauki A Yankunan Su

Written by Admin

Daga: ZAHARADEEN SALEH

Al’ummar garuruwan ‘Yar Gaya, Dadin Kowa, Jido da Kuma Marmaraje dake yankin karamar hukumar Dawakin Kudu sun roki gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da ya kawo musu dauki saboda yinkurin kwace musu gonaki da wasu mutane ke kokarin yi.

Al’ummar, sunyi wannan roko ne a lokacin da suka gudanar da wata zanga-zangar lumana saboda rashin amincewar su a kokarin kwace musu gonaki da ake yi.

Daya daga cikin mutane da suka yi bayanin, Malam Bashir Bello ‘Yar Gaya, ya bayyana cewa suna rokon mai girma gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf daya kawo musu daukin gaggawa saboda wannan fin karfi da ake yinkurin yi musu.

Bashir ‘Yar Gaya yace, sun wayi gari sun ga wasu mutane suna auna musu gonaki, kuma sun tambaye su amma suka ce su jira nan gaba za’a yi musu bayani.

Wata mata mai suna Talle Ali tace “tana kira ga gwamnan ya taimake su mijin ta ya mutu ya barta da ‘ya’ya ashirin, da wadanan gonaki suka dogara dasu suke ci suke sha amma ana so a kwace musu.”

Shi ma ana sa jawabin mai unguwar ‘Yar Gaya Haruna Hassan da yayi bayanin amadadin masu unguwannin garuruwan yace “basu san komai ba akan wannan al’amari.”

Haruna Hassan ya kara da cewa “akwai bukatar gwamnan Kano ya kawo musu dauki domin kubutar da al’ummar wadanan garuruwan daga halin firgici da suka samu kan su a ciki.

Leave a Comment