Muhalli

Allah Ya Isa Ga Masu Zuba Mana Shara A Tsakiyar Titin Kabara — Kabiru Getso

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah ya Isa ga wasu mutane da ta bayyana a matsayin marassa kishin cigaban al’umma kan yadda suke zubar da Shara a Tsakiyar Titinan birnin Kano musamman masu a Unguwar Kabara bayan gidan Sarki da ke yankin karamar hukumar birni da Kewaye.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin tsaftar Muhalli da ake gudanarwa a duk Asabar din karshen wata a nan Kano.

Kabiru Getso ya ce zubar da sharar da wasu mutane suke yi ba bisa ka’ida ba musamman a kan titunan kwaryar birnin Kano alama ce da ke nuna halin ko-in-kula a sha’anin kula da lafiyar al’umma, kuma dabi’ar ka iya janyo yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma.

Ya ce yadda wasu marassa kishi suka zubar da shara akan titin kabara abin Allah wadai ne kuma gwamnatin jihar Kano ba zata zuba ido hakan ta cigaban da faruwa ba.

“…Ina so idan kun gama wannan aikin kuje Kabara wajen Transformer nan ku gani tsakanin gidan Malam Nasiru Kabara da gidan Mai martaba Sarkin Kano ku gani, wani bala-gurbi, wani marar kishin jihar Kano, marar kishin Al’umma ya je Tsakiyar titi ya zuba mana shara, inda ba gurin zuba shara bane, kusan a satin nan ina Jin munje mun kwashe shara a gurin nan ya kai sau uku, kuma yasan ce, ko sun san cewa ba gurin Zuba shara bane, to amma an zuba shara a gurin ko Dan a muzanta mana, ko Dan a batawa gwamnati ne, Allah wadai ko waye wannan, Allah ya biwa Al’umma hakkinsu, saboda baza mu rika kyale wannan ba, bamu yafe ba, Allah ya Isa Wanda yayi mana wannan, saboda cutar da al’umma ne wannan, duk Mai son cigaba ba zai zo ya Zuba shara akan titi ba”, Inji Kabiru Getso.

Ya kuma yabawa kungiyar cigaban Dan-agundi Mu taimaki Juna mai lakabin DAMJUDA bisa yadda suke bada gudun mowa wajen kula da muhalli musamman a lokacin tsaftar muhalli ta wannan watan.

Ku karanta: Tsaftar Muhalli: An ci Tarar Tashar Motar Rijiyar Zaki Dubu 100, Kowacce Mota Dubu 10

A jawabinsa, shugaban kungiyar DAMJUDA Kwamared Musaddiq Kafinta ya yabawa maaikatar muhalli yayi inda ya bada tabbacin kungiyar na cigaba da aiwatar da ayyukan kula da tsaftar muhalli.

A lokacin tsaftar Muhallin, kotun tafi da gidan ka ta tsaftar muhalli ta jihar Kano ta kama mutane 80 da lefin karya dokar inda aka yi musu tarar naira dubu 70 da 400.

Leave a Comment