Yanzu-Yanzu

Alh.Bello Idi ya zama kaigaman Kano

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sake nada wasu sababbin hakimai guda hudu tare da daga Darajar wasu Hakiman guda shida.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ta rawaito Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero na cewa an nada su Sarautun ne bisa cancanta da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Wadanda aka nada din sun bhadar da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Dan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.

Sai kuma Hakiman da aka ciyar da su gaba sun hada da Malam Umar Sunusi Bunun Kano ya koma Dan Makwayyon Kano da Malam Ibrahim Hamza Bayero Dan Madamin Kano zuwa Dan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.

Sauran Hakiman da aka ciyar da su gaba sune Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zannan Kano zuwa Dan Madanin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Dankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya hore su da su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikin su da gaskiya da amana tare da Sanya tsoron Allah a duk al’amuran su.

Leave a Comment